Police Recruitment

Police recruitment for Constable opening on 14th July 2020

Ga masu sha’awar shiga aikin dan-sanda, matakin CONSTABLE kawai, za’a fara online application ranar Talata, 14th July, za kuma a rufe application 23rd August. Ga sharadi (Requirements) kamar haka:

  1. Ana bukatar matasa daga shekara 17 zuwa 25

  2. Yazama kuna da email wanda yake aiki

  3. Ana bukatar 5 credits cikinsu harda maths da English.

  4. Ana bukatar National Identification Number (NIN). Idan baka da shi ka tambaya inda akeyi, kyautane kaje marmaza kayi kamin 14th July dan kacika sharadi.

  5. Dole kazama mai koshin lafiya.

Idan ka cika wadannan sharadai na sama, sai ka jira ranar 14th July wannan website: www.policerecruitment.gov.ng zai fara aiki. Ka bude ka cike form. Ana bukatar kai printing form bayan ka gama cikewa, kai printing email confirmation da zaa turo maka da kuma registration number; kai printing guarantors form shima saboda zaa a bukacesu ranar da kazo interview.

Wadanda suke da sha’awa amma basu da kudin zuwa internet cafe, zamu fito tsari na tallafa musu nan gaba kadan.

NAM